Jihohin da za su Samun Ruwan Sama Mai ƙarfi na Tsawon Kwana 3 a Faɗin Najeriya – NiMet
Hukumar kula da yanayin samaniya ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen samun ruwan sama kamar da bakin ƙwarya gami da tsawa daga yau Talata har zuwa ranar Alhamis a fadin ƙasar.
Hasashen yanayin da NiMet ta fitar a Abuja ya ce akwai yiwuwar samun yanayin hadari mai ƙarfi a ranar Talata da kuma raguwar hasken rana a yankin arewacin ƙasar.
Read Also:
Hasashen, ya kuma ce ana iya samun ruwan sama da tsawa da safe a wasu jihohin arewa kamar Adamawa da Taraba da Sokoto da Zamfara da Katsina da Kebbi da kuma Kaduna,
Sannan da rana, mai yiwuwa za a yi ruwan sama da tsawa a sassan jihohin Bauchi da Gombe da Adamawa da Taraba da Kaduna.
A jihohin Kudu da na kusa da teku kuma, mai yiwuwa za a yi ruwa da tsawa da safe a jihohin Osun da Oyo da Ekiti da Ogun da Legas da Akwa Ibom da Ribas da Bayelsa da kuma Cross River.
A ranar Laraba, yankin arewa zai iya fuskantar baƙin hadari da dusashewar hasken rana inda hukumar ta yi hasashen samun ruwa da tsawa da safe a sassan jihohin Adamawa da Taraba da kuma Gombe.