Fasinjoji 20 Sun Mutu a Hatsarin ƙwale-kwale a Jihar Neja

 

Aƙalla mutum 24 galibinsu manoma ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka ɓace a lokacin da wani ƙwale-kwale ɗauke da fasinjoji ya kife a garin Gbajibo, a ƙaramar hukumar Mokwa da ke jihar Neja a arewa ta tsakiyar Najeriya.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi.

Rahotonni na cewa fasinjojin kwale-kwalen sun fito ne daga garuruwan Gbajibo da Ekwa da Yankeiade.

Jaridar Daily a Najeriya ta ambato shugaban ƙaramar hukumar Mokwa Jibrin Abdullahi Muregi na cewa an kuɓutar da gawarwaki 21.

Jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce suna tattara alƙaluma domin sanin haƙiƙanin adadin mutanen da lamarin ya shafa.

Hatsarin na zuwa ne kwana biyu bayan da wani kwale-kwale ya kife ɗauke da fasinjoji ciki har da mata da ƙananan yara ya kife a Yola ta jihar Adamawa, lamarin da ya haddasa asarar rayuka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com