Ban Ki-Moon ya Jinjina wa Shugaba Buhari Game da Shawo Kan Matsalar Tsaro

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nuna jin dadi kan kalaman da tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kan rawar da gwamnatinsa ta taka wajen inganta tsaro da bunkasa tattalin arzikin kasar.

A jiya ne dai Shugaba Buhari da Ban Ki-moon suka tattauna ta wayar tarho, Buhrin ya jaddada girman da Mista Moon ke da shi a wurinsa, tare da gode masa kan wayar tarhon da ya yi, a cewar wata sanarwa da fadar gwamnatin Najeriya ta fitar.

Sanarwar da mai bai wa shugaban shawara kan yada labarai Malam Garba Shehu ya sanya wa hannu, ta ce Moon ya jinjina wa Shugaba Buhari game da shawo kan matsalar tsaro da kasar ke fama da ita.

Garba Shehu ya ce shugaban ya gode wa tsohon Magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar kan gudunmawar da ya bai wa Najeriya a lokacin da yake kan aiki.

Mista Moon ya kuma gode wa shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya Farfesa Ibrahim Gambari da ya taba aiki karkashin sa, da kuma Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Hajiya Amina Muhammad, wadanda ya ce shekarun da suka yi aiki tare masu muhimmanci ne da kokarin kawo ci gaba a Najeriyar.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya, musamman arewacin kasar da ke fama da matsalar barayin daji, da masu satar mutane don neman kudin fansa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here