2023: Goodluck Jonathan na Iya Kara Neman Tikitin Shugaban Kasa
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya ce Jonathan zai iya fafutukar neman tikitin tsayawa takara a 2023 karkashin jam’iyyar.
A cewarsa, kin amsa gayyatar majalisar tarayya da Buhari yayi, alama ce da ke nuna yayi burus da ‘yan Najeriya.
Ya kara da cewa, masu guduwa daga jam’iyyar PDP zuwa APC suna saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Prince Uche Secondus, Shugaban jam’iyyar PDP na Najeriya ya ce Jonathan zai iya fafutukar neman tikitin tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar.
Sauran jiga-jigan jam’iyyar masu ra’ayin tsayawa takarar za su iya yakin neman tikitin, kamar yadda shugaban jam’iyyar yace, The Nation ta wallafa.
Secondus ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari a kan kin amsa gayyatar majalisar tarayya, wacce ta bukaci yayi magana a kan matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan.
Read Also:
A cewarsa, rashin amsa gayyatar majalisar kamar share gaba daya mutanen Najeriya ne, saboda su suka zaba a matsayin wakilansu.
Secondus ya ce rashin amsa gayyatar tasa alama ce da take nuna cewa ba shi da wani abu da zai fadi a kan kokarin gyara harkokin rashin tsaron da ke kasar nan.
A cewarsa, “Wannan kame-kamen da shugaban kasa yake yi alama ce wacce take nuna cewa ya gaza a shugabancinsa.
“Yin burus da wakilan jama’a kamar share gaba daya ‘yan Najeriya ne.
A gaskiya, hankula a tashe suke, shugaban kasa bai damu da damuwarmu ba, idan ba haka ba mai zai sa ya kasa fuskantar jama’a yayi musu bayani?
“Babbar matsalar mu a yanzu shine yadda gaba daya Najeriya ta lalace, kuma gwamnati bata da niyyar yin komai a kai.”
Ya kara da cewa duk wadanda aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP suka koma jam’iyyar APC sun aikata abinda bai dace ba.Sannan yakamata majalisar tarayya dauki mataki a kansu, saboda hakan ya saba wa doka.
A cewarsa, “Ba na tunanin shugabannin majalisar tarayya suna amfani da kundin tsarin mulkin kasar nan. Idan da suna yi, da basu bari ana wannan canje-canjen jam’iyyar ba.”