Kano:  Yadda Wasu Bursunoni Suka Samu Yanci

 

Akalla Bursunoni 37 sun samu yanci ranar Alhamis a jihar Kano.

Hakan na cikin yunkurin gwamnatin tarayya na rage cinkoso a gidajen gyara hali.

Kundin tsarin mulki ya baiwa Alkalin Alkalai dama ‘yanta Bursunoni Alkalin Alkalan jihar Kano, Nura Sagir Umar, ya ‘yantar da Bursunoni 37 dake gidajen yarin jihar domin rage cinkoson dake ciki bisa manufar gwamnatin tarayya.

Jawabin da Kakakin hukumar gyara halin jihar, DSC Musbahu Lawal, ya ce an tsawatar da wadanda aka saki kuma an shawarcesu su kasance mutanen kirki kuma suyi amfani da daman wajen yiwa kawunansu abubuwan arziki.

Bayan haka an baiwa kowanne cikin N2,000 matsayin kudin mota domin su koma wajen iyalansu, Daily Trust ta ruwaito.

A bangarensa, kwantrolan hukumar gidajen gyara hali na jihar, Suleiman Suleiman, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Yunusa Lawan, ya yi kira ga Bursunonin su nisanci abubuwa laifi kuma su kasance masu bin doka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here