Majalisar Tarayya ta yi Korafin Rashi Zuwan Shugaba Buhari

 

Majalisar tarayya ta ce bata gayyaci Buhari don ta kure shi ba.

Ta so su tattauna ne a kan matsalolin tsaro da ke damun Najeriya.

Ta kara da cewa mafi yawan ‘yan majalisar ‘yan jam’iyyarsa ne.

A ranar 1 ga watan Disamba, majalisar tarayya ta gayyaci Buhari don tattaunawa a kan harkokin tsaro, bayan ‘yan Boko Haram sun kashe wasu manoman shinkafa a jihar Borno.

Gayyatar da majalisar ta yi wa Shugaban kasa ta janyo cece-kuce iri-iri, saboda wasu daga cikin ‘yan majalisar sun wajabta wa Buhari amsa gayyatar.

A ranar 4 ga watan Disamba, Femi Gbajamiala, kakakin majalisar ya bayyana cewa Buhari ya amince da zama da majalisar.

Murna ta koma ciki ne a ranar Laraba, bayan Abubakar Malami, Antoni janar na gwamnatin tarayya, ya ce majalisar tarayya ba ta da hurumin gayyatar shugaban kasa a kan ayyukan jami’an tsaronsa.

Kakakin majalisar, ya ce Shugaban kasa bai fi karfin jam’iyya ba, tunda mafi yawan ‘yan majalisar ‘yan jam’iyyar APC ne.

Kalu ya fadi hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, inda yace majalisar ta bukaci zaunawa da shi don tattaunawa a kan matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here