Jose Mourinhi Ya Fadi Sabon Inkiyar sa

 

Mai kula da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham, Jose Mourinho ya ce baya son tsohon laƙabinsa na ‘Special One’.

Ya bayyana cewa daga yanzu yana son a rika masa inkiya da sabon laƙabin ‘Experienced One’, ma’ana wanda ya ƙware.

Mourinho ya ce duba da tarin shekarun da ya yi ana damawa da shi a harkar kwallon ƙafa, ya samu gogewa da ƙwarewar da ya cancanci sabon laƙabin.

Jose Mourinho ya raɗa wa kansa sabon inkiya inda ya bayyana cewa yana son a dena kiransa da lakaɓin ‘Special One’.

Jose Mourinho wadda tun shekarar 2004 ake dama wa da shi a gasar Premier ya bayyana cewa laƙabin ‘Special One’ ta tsufa.

Amma a yanzu ya ce yana son a dinga kiransa da laƙabin ‘Experienced One’, kamar yadda LIB ta ruwaito.

Fitaccen cocin ɗan ƙasar Portugal ya jagoranci Tottenham zuwa Premier League karo na biyu kuma ana yi wa tawagarsa kallon ɗaya daga cikin wadanda za su iya zama zakaru a gasar.

Mourinho ya naɗa wa kansa laƙabin ‘Special One’ a shekarar 2004 a yayin da ya ke tashe sosai a Chelsea.

Tun daga wannan lokacin laƙabin na ‘Special One’ ke binsa. Amma a ranar Alhamis 19 ga watan Nuwamban 2020 ya bayyana sabon sunan da ya ke so.

“The Experienced One.’ Na goge sosai yanzu, “Mourinho ya bawa manema labarai amsa da suka tambaye shi sunan da ya ke so yanzu.

“A yanzu galibi ba wani sabon abu da ke faruwa da Ni a ƙwallo da ban taɓa ganin makamancinsa ba.

“Akwai ayyukan da ke buƙatan kuzari kamar ɗan wasan ƙwallo, Ɗan shekara 40 ba zai iya samun kuzari irin ta ɗan shekara 20 ko 30 ba, idan dai kai ba Zlatan Ibrahimovic bane.

“Amma aikin coci ƙwaƙwalwa kawai ka ke buƙata, daɗewa kana aikin yana sa ka koyi darussa kuma ka ƙara goge wa”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here