Jagoran Juyin Mulki a Gabon ya Kare Matakin da Sojoji Suka ɗauka na Kawo Karshen Mulkin Shugaba Bongo
Janar din sojin da ya jagoranci juyin mulki a Gabon kuma shugaban gwamnatin riƙo, ya kare matakin da sojoji suka ɗauka na kawo karshen mulkin shugaba Ali Bongo.
Read Also:
Janar Oligi Ngwema, ya shaidawa jaridar Le Monde ta Faransa cewa Mista Bongo ba shi da damar yin mulki a wa’adi na uku, sannan zaɓen da aka gudanar a makon da ya wuce cike ya ke da kura-kurai.
Man Foumbi shi ne kakakin shugaban riƙon wanda ya shaidawa BBC cewa Janar Oligi Ngwema ya umarci a mayar da layukan intanet da gidajen Talbijin na gida da ƙasashen waje.
A wannan Alhamis din ‘yan Gabon za su iya fita harkokinsu daga karfe 6 na safiya zuwa 6 na yamma.
Mista Bongo da mahaifinsa dai sun jagoranci ƙasar Gabon na tsawon shekaru 53.