An kaddamar da Littafin ‘Boko Halal’ a Borno
Wata gidauniya ta Allamin mai zaman kanta a birnin Maidugurin Borno ta kaddamar da wani littafi mai suna Boko Halal domin daƙile al’adar kaifin kishin islama.
Boko Halal da fari an soma rubuta shi da Ingilishi kafin daga bisani aka fassara zuwa harshen Hausa da Kanuri.
Sunan da aka bai wa littafin, da ke nufin babu haramci a koyon ilimin Boko, kai-tsaye na yakar akidar Boko Haram.
Shugabar gidauniyar, Hamsatu Allamin, ta shaida cewa bijiro da wannan manufa yayinda ake cika shekaru 12 da rikicin Boko Haram za ta koyar da mutane kan ainihin sakonni addinin musulunci.
A shekara ta 2016 aka soma bijiro da littafin Boko Halal kafin sauran kungiyoyi su sake nazartar littafin da shawarwarinsu.
Gidauniyar ta ce manufarta shi ne jan hankali yara masu tasowa da dasa musu dabi’u masu alfannu ga cigaba al’umma.