Jahar Kaduna Zata Datse Layukan Sadarwa a Sassan Jahar
Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sanar da al’ummar jaharsa cewa su shirya
ya domin za a katse layukan sadarwa a kokarin da jami’an tsaro ke yi na kaddamar da hari kan ‘yan bindiga da ke buya a wasu kananan hukumomi.
Gwamna El-Rufai ya ce katse layukan ba zai shafi duk jahar ba, amma wasu sassan na jahar kamar kananan hukumomin da ke iyaka da Zamfara da Katsina za a katse layukansu.
Read Also:
Elrufai ya ce kaste layukan da aka yi a jahohin Zamfara da Katsina ya bai wa ‘yan bindiga damar kutsa kai wasu kauyukan makwabtan jahohi kamar Kaduna domin amfani da layukan waya don amsar kudin fansa.
Ya kara da cewa tuni ya aike wa gwamnatin tarayya wannan bukata wanda ya ce shugaba Buhari ya amince da matakin.
Yankunan Birnin Gwari da Giwa da Chikun da Igabi da Kajuru da Kachia su ne suka fi fuskantar barazana daga hare-haren ‘yan bindiga.
Sannan gwamnan ya ce tuni gwamanati ta kaddamar da rundunar kar-ta-kwana da za ta ke zagaye a kowanne sassa domin tabbatar da cewa mutane na bin dokokin da aka kafa domin dakile ‘yan bindiga.