Kaduna: Gwamnatin ta Sassauta Dokar ta Baci a Wasu Kananan Hukumomin Jahar 

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya kakaba dokar ta baci ta tsawon 24 a dukkan kananan hukumomin jihar

An saka dokar takaita zirga-zirga a fadin jihar Kaduna ne biyo bayan barnatar da kayan tallafin korona da batagarin matasa ke yi a sassan Najeriya – Mista Samuel Aruwa, kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na Kaduna, ya sanar da sassauta dokar ta bacin a kananan hukumomi 21 Gwanatin jihar kaduna ta karbi shawarar hukumomin tsaro na sassauta dokar ta baci a kananan hukumomin jihar guda 21. Sai dai, dokar ta baci ta tsawon 24 za ta cigaba a kananan hukumomin Chikun da Kaduna ta kudu har zuwa sanarwa ta gaba da za a fitar ranar Talata, kamar yadda kwamishinan tsaron cikin gida na Kaduna, Mista Samuel Aruwan, ya sanar
A cikin sanarwar, Mista Aruwan ya bayyana cewa; ”jama’a zasu iya fita harkokinsu na yau da kullum daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 4:00 na yammacin kowacce rana daga ranar Talata, 27 ga watan Oktoba, a kananan hukumomi 21. “Dokar ta baci ta tsawon sa’a 24 tana nan daram a kanan hukumomin Chikun da Kaduna ta kudu”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here