Majalisar Dokokin Jahar Kaduna ta Tsige Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Haruna Inuwa
‘Yan majalisar dokokin jahar Kaduna sun tsige Haruna Inuwa, shugaban masu rinjaye na majalisar.
An tsige Inuwa ne a ranar Laraba bayan da ‘yan majalisa na APC 17 suka rattaba hannu kan takardan tsige shi.
Tanimu Musa, Shugaban kwamitin sadarwa na majalisar ya ce nan gaba za su sanar da sabon shugaban masu rinjaye.
Kaduna – Majalisar dokokin jahar Kaduna ta tsige Haruna Inuwa, shugaban masu rinjaye na majalisar, The Cable ta rawaito.
Read Also:
An tsige Inuwa, mai wakiltar mazabar Doka/Gabasawa ne a ranar Laraba kamar yadda Leadership ta rawaito.
An cimma matsayar hakan ne bayan da mambobin majalisar suka jefa masa kuri’an rashin amincewa da jagorancinsa.
‘Yan majalisar APC 17 sun ratabba hannu kan wasikar tsige shi A cewar kamfanin dillancin labarai na NAN, mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) su 17 ne suka rattaba hannu kan wasikar tsige shi.
Da ya ke magana da manema labarai jim kadan bayan zaman majalisar, Tanimu Musa, Shugaban kwamitin sadarwa na majalisar, ya ce kan yan majalisar ya hadu wurin kuri’un rashin amincewar.
Ya ce:
“Don haka, Mabo zai kasance tsigagen shugaba har zuwa lokacin da za a sanar da sabon shugaban masu rinjaye.