Tsohon shugaban NCAA Kaftin Mukhtar Usman ya Rasu
Kaftin Mukhtar Usman, tsohon shugaban hukumar NCAA, ya rasu a daren ranar Talata a asibiti.
Ilitrus Ahmadu, shugaban wata kungiyar harkar sufurin jiragen sama, ya tabbatar da rasuwar Kaftin Usman da safiyar ranar Laraba.
An haifi marigayi Kaftin Usman a ranar 5 ga watan Disamba na shekarar 1956.
Tsohon babban darekta a hukumar NCAA (Nigerian Civil Aviation Authority), Kaftin Mukhtar Usman, ya rasu, kamar yadda jaridar Punch ta tabbatar a cikin rahoton da ta wallafa.
Kaftin Usman ya rasu a daren ranar Talata a Zaria bayan takaitacciyar rashin lafiya.
Read Also:
Ya rasu ya na da shekaru 63 a duniya.
Punch ta rawaito cewa Ilitrus Ahmadu, shugaban wata kungiyar harkar sufurin jiragen sama, ya tabbatar mata da rasuwar Kaftin Usman da safiyar ranar Laraba.
“Yanzu na ke samun labarin mutuwarsa. An garzaya da shi zuwa asibiti a daren jiya (Talata) a Zaria, jihar Kaduna, kafin daga bisani ya ce ga garinku nan,” Kamar yadda Ahmadu ya sanar da Punch ta wayar tarho.
Kafin ya zama babban darektan NCAA, Kaftin Usman ya taba rike mukamin kwamishina a hukumar binciken hatsarin jirgin sama.
Kazalika, ya taba rike mukamin manajan darekta a tsohon kamfanin sufurin jiragen sama na Najeriya.