Kungiyar IMAK ta Kalubalanci Masu Son a Rushe Masarautun Kano

 

Wata kungiya mai suna Inuwar Masarautun Kano Biyar (IMAK) ta yi kira ga majalisar dokokin jihar Kano da ta yi watsi da rokon wata kungiya mai suna ‘Yan Dagwalen Kano – wadda a baya-bayan nan ta bukaci a rusa masarautun jihar guda hudu tare da mayar da tsohon sarki Khalipha Sanusi Lamido Sanusi.

Kiran na kunshe cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ta IMAK, Nasiru Ibrahim Rano ya aike wa shugaban majalisar dokokin jihar Kano.

Kungiyar ta IMAK ta ce rushe masarautun kamar mayar da hannun agogo baya ne duba da rawar da suke takawa wajen samar da ci gaba ga al’ummarsu.

Sanarwar ta bayyana illar rushe masarautun da ta ce yin hakan ka iya rikidewa zuwa matsalar tsaro da za ta jefa rayuka da dukiyoyin jama’a cikin wani hali.

A cewarta, kyale masarautun zai ba da dama wajen farfado da martabarsu wanda hakan hanya ce da za ta taimaka wajen gaggauta aiwatar da manufofin gwamnati.

Ta kara da cewa ana girmama duka sarakunan inda sanarwar ta ce a shirye suke su yi iya karfinsu domin tabbatar da zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki a jihar Kano.

“Babu wani sarki da aka taba samu da hannu a cin hanci da rashin da’a ko yin ba daidai ba, a don haka kyale su a kan mukamansu shi ne abu mafi dacewa a wannan lokaci.” kamar yadda sanarwar kungiyar ta bayyana.

A karshe kungiyar ta yi kira ga majalisar dokokin da ta saurari bukatarsu ta kuma duba kiran saboda zaman lafiya a Kano.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com