Matatar Man Ɗangote za ta Fara Sayar da Fetur
Matatar mai ta Dangote za ta fara sayar da man fetur a Najeriya, a cikin makonni masu zuwa.
Kamfanin dillancin labarai na Rauters ya ce wasu majiyoyi a kamfanin sun tabbatar masa da hakan, a ƙoƙarin da aka jima ana yi, na ganin Najeriya ta dogara da kanta a ɓangaren makamashi.
Rauters ya ce ana sa ran fara sayar da man fetur ɗin ‘kowane lokaci daga yanzu’.
Read Also:
Hakan dai na nuni da cewar akwai yiwuwar Najeriya za ta rage yawan man fetur, da kuma man disel domin harkokin yau da kullum, daga manyan kamfanonin sayar da mai, da take shigar da shi, wata harka da ta ƙunshi biliyoyin nairori da aka jima ba a iya magance ta ba.
Haka kuma wata majiya ta shaida wa Rauters cewar kamfanin samar da man fetur a Najeriya NNPC, ya ce zai samar wa matatar ta Ɗangote ɗanyen mai ganga miliyan huɗu a watan Maris, wanda hakan ke nufin, matatar Ɗangoten ta karɓi ɗanyan man fetur ganga miliyan 12 tun daga watan Disambar, bara.