Ba abu ne Mai Yiwuwa ba a Zartar da Dukkan Buƙatun NLC – Gwamnatin Tarayya

 

Gwamnatin Najeriya ta ce ba abu ne mai yiwuwa ba a zartar da wasu daga cikin bukatun kungiyar kwadago da aka cimma a watan Oktoban 2023, da gaggawa ba.

Karamar ministar kwadagon kasar, Nkeiruka Onyejeocha ce ta shaida wa ‘yan jaridu a yau Juma’a yayin amsa tambayoyi ga ‘yan jaridun.

Gwamnatin ta tarayya ta kara da cewa daya daga cikin yarjeniyoyin wadda take neman a samar da cibiyoyin sauya motoci zuwa masu amfani da iskar gas zai dauki lokaci kafin cibiyoyin su wadata ko’ina kuma kwamitin da ke kula da samar da cibiyoyin yana aiki tukuru.

A watan Oktoban bara ne dai bangarorin biyu suka cimma jerin yarjejeniyoyi da suka kunshi ragewa ‘yan kasar radadin talauci sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi.

Sauran bukatun sun hada da samar da mafita ga darajar naira da tashin farashi da kuma matsalar tsaro da dai sauransu.

Kungiyar kwadago dai ta bai wa gwamnati wa’adin mako biyu da ta zartar da yarjeniyoyin ko ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com