Abuja: An kama Wani Dan Tsohon Ministan Najeriya
An cafke dan wani tsohon ministan Najeriya daga jihar Benue a yayin da ya tafi fashi da makami a Abuja.
Dan tsohon ministan ya dauki daya daga cikin motocin mahaifinsa ne ya kuma tafi da bindiga don satar kudi a wurin ‘yan canjin kudi na Abuja – A yayin yunkurin fashin ne wani daga cikin ma’aikatan wurin ya kama shi inda daga bisani aka mika shi hannun ‘yan sanda An kama ɗan wani tsohon minista a Najeriya kan zargin yunkurin fashi da makami a wurin canjin kuɗi a Abuja.
An ruwaito cewa wanda ake zargin ya yi yunkurin fashin ne a makon da ta gabata. A halin yanzu yana tsare hannun hukuma inda ake cigaba da bincike kamar yadda The Nation ta ruwaito. Majiyar ta gano cewa wanda ake zargin ɗan wani tsohon minista ne daga Jihar Benue.
Read Also:
Wani majiya da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, “Tsohon ɗan ministan ya kutsa wurin canjin kuɗin makon da ya wuce a Abuja ɗauke da bindiga don ya yi fashin kudi. A cikin motar mahaifinsa ya tafi wurin.
“A yayin da ya ke sata a wurin, ɗaya daga cikin masu aiki a wurin ya kama shi ya masa duka kafin ya mika shi hannun ƴan sanda. Fusatattun matasa sun koma fasa motar mahaifinsa da ya tafi satar da ita.’
“Binciken farko da aka gudanar ta tabbatar da cewa wanda ake zargin, ma’aikacin hukumar gwamnatin tarayya ya saba da rayuwar almubazaranci. “Ƴan uwansa na ta kai da komowa don ganin sun daidaita da mai canjin kuɗin don a sako shi. “Ana ta ƙoƙarin yin rufa-rufa kada abin ya fito fili.”
A halin yanzu dai rundunar ƴan sanda ba ta fitar da sanarwa a game da fashin ba. Amma majiyar ya ce: “da gaske ne an kama shi kan zargin fashi a wurin canjin kuɗi kuma yana hannun hukuma. “Jami’an mu na masa tambayoyi. Bisa alamu ya san abinda ya aikata kuma babu alamar cewa yana cikin maye.