An Kama Fasto Mai Sheharu 70 Bisa Laifin Damfara, Ha’inci da Sata
An maka wani fasto mai shekaru 70 a kotu bayan ya lamushe N870,000 da sunan zai samar da man sihirin da ake amfani da shi wurin wanke daloli.
Fasto Emmanuel Bello, mazaunin Idimu, ya bayyana a gaban kotu bisa zargin da ake masa na ha’inci har da amsar kudade da kuma sata.
Ya amshi kudin ne daga hannun Bilkisu Ilabisi kuma ya kasa samar da man sihiri, kuma an yi kokarin amsar kudaden daga hannunsa amma ya murje ido ya ki bayarwa.
Jahar Lagos – An maka wani fasto mai shekaru 70 a kotu bayan ya amshe N870,000 da sunan zai sayo ‘man sihiri’ wanda ake amfani da shi wurin gyara daloli da wanke su.
Daily Trust ta rawaito cewa, Emmanuel Bello, mazaunin Idimu, ya bayyana a gaban kotun majistare da ke Ikeja a jahar Legas don ana tuhumar shi da laifin ha’inci na amsar kudade da yaudara har da sata.
Read Also:
An gabatar wa da kotun yadda Bello ya warwari kudade daga hannun Bilkisu Olabisi bayan ya yi mata alkawarin samo mata man sihiri wanda ake amfani dashi wurin wanke daloli da tsaftace su.
Wanda ake zargin tare da wasu sun aikata laifin a ranar 2 ga watan Maris a wuraren Idimu da ke jahar Legas, kamar yadda sifeta Mojkrade Edeme ya sanar da kotu.
Bayan ya amshi kudaden daga hannun ta, ta yi iyakar kokarin ganin ta karbi kudin daga hannunsa amma hakan ya ci tura. Shiyasa ta kai kararsa don a damke mata shi, a cewar dansandan.
Laifin da ya tafka ya ci karo da sashi na 287, 314 da 411 na dokar laifukan jahar Legas na 2015, Daily Trust ta rawaito.
Bangare na 287 sun sanya hukuncin ya zama shekaru 3 a gidan gyaran hali, sannan bangare na 314 ta yanke shekaru 15 sakamakon amsar kudade bisa karya.
Alkalin kotun O.O Raji, ya bayar da belin mai laifi ya zama N100,000 da kuma tsayayye guda daya.
Raji ya ce wajibi ne tsayayyen ya kasance mai aiki mai kyau, sannan ya gabatar da shaidar biyan kudin haraji na shekaru biyu ga gwamnatin jahar Legas.