ƙasar Amurka ta Kwashe ‘Yan ƙasarta 1,200 Daga Afghanistan

 

Amurka ta kwashe ƴan ƙasarta 1,200 daga filin jirgin saman Kabul a jiya Lahadi, a cewar wata sanarwa da fadar White House ta fitar yau Litinin, yayinda ta kawo karshen aikinta na kwashe mutananta.

Wannan adadi bai kai rabin wadanda aka kwashe a sa’o’i 24 baya ba, kuma ya nuna ragin da aka samu yayinda Amurka ke shirin ficewa baki ɗaya daga Afghanistan a ranar Talata.

Zuwa yanzu dai kusan mutum dubu 120 aka kwahe baki ɗaya daga Afghanistan tun 14 ga watan Agusta, kwana guda kafin Taliban ta karɓe birnin Kabul.

Akasarin sauran kasashen, ciki harda Burtaniya tuni sun janye dakarunsu da dakatar da kwashe mutane daga filin jirgin saman Kabul.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here