Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga Sama da 50 da Lalata Makamansu a Jahar Zamfara

 

Sojoji sun fatataki ƴan bindiga daga ginin wata makaranta da ke karamar hukumar Shinkafi a jahar Zamfara a wasu hare-haren sama.

Hare-haren da suka kai ta jiragen yaƙi sun shafi yankunan Zangon Dammaka da Jajaye maboyar wani fitaccen ɗan bindiga Kachalla Haru da yaransa.

Ɗaya daga cikin dakarun hadin-gwiwar da suka kai harin a Zamfara ya shaidawa Jaridar PRNigeria cewa sun yi nasara a dukkanin samamen da suka kai a karshen mako.

A cewar dakarun anyi nasarar kashe ƴan bindiga da dama da lalata makamansu. Sannan an lalata dazukan da suke ɓuya a Sububu.

Wata majiya ta tabbatarwa PRNigeria cewa an kashe sama da ƴan bindiga 50 da lalata makamansu da babura a kauyen Gidan Rijiya.

guest post service provider

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here