An Kama na Hannun Daman Kasurgumin Shugaban ‘Yan Bindigan Zamfara, Kachalla
Hukumar DSS ta sanar da cewa ta kama wasu masu yi wa yan bindigan Zamfara safara makamai.
Wanda aka kama din shine wani Aliyu Yahaya da ake ce na hannun daman kasurgumin shugaban yan bindiga, Kachalla Damina ne.
Kakakin DSS, Peter Afunanya ya lissafa bindigu da harsashi da gurneti da wasu makamai da aka samu tare da wanda ake zargin.
Zamfara – Hukumar tsaron farin kaya, DSS, ta ce ta kama wani Aliyu Yahaya mai safarar bindigu kuma na hannun daman Kachalla Damina, kasurgumin dan bindiga da ake zargi yana adabar mutanen Dansadau da kewaye a Zamfara.
Mai magana da yawun hukumar ta DSS, Peter Afunanya ne ya sanar da hakan yayin wata jawabi da ya yi a ranar Alhamis, The Cable ta rahoto.
Read Also:
Afunanya ya ce kayayakin da ako kwato hannun Yahaya sun hada da:
“Bindiga kirar GPMG guda daya, charbi na harsashi, harsashi na GMPG guda 190, harsashi na AK 47 guda 28 da gurneti guda daya.”
Ya kuma cigaba da cewa a Kaduna, an kama yan aiken yan bindiga – Tukur Usman da Iliyasu Adamu a karamar hukumar Chikun a ranar 20 ga watan Fabrairu, ya kara da cewa an samu harsashi guda 372 masu tsawon 7.62 X 39mm da harsahi na GPMG guda 26 a hannunsu.
Ya ce wadanda ake zargin suna daga cikin masu sayarwa yan bindigan jihar Zamfara makamai, kuma an fara kama su ne a ranar 22 ga watan Janairu a hanyar Barkin Ladi – Pankshin, a jihar Plateau suna hanyar kai wa kwastomominsu makaman.
Afunanya ya ce an kwace harsashi 612 na GPMG 120 da AK-49 da suka boye a cikin buhun shinkafa a hannunsu a lokacin.