Kama Imran Khan ya Saɓa Doka – Kotun Koli
Kotun koli a Pakistan da ta umurci hukumomi da su gabatar da tsohon Firaiminista Imran Khan wanda ke tsare a gaban Alkalai a wannan Alhamis din, ta ce an saɓa doka wajen kama shi.
Kotu ta bukaci a gaggauta sakinsa.
Tun da fari dama dai lauyoyin Mista Khan sun yi korafin cewar tsare shi da a ka yi a harabar babbar kotu ranar Talata ba daidai ba ne.
Alkalin Alkalan Pakistan ya nemi sanin dalilin kama mutum a harabar kotu.
Read Also:
Kamen Mista Khan ya haifar da bore daga magoya bayan sa a fadin kasar, ana cigaba da tsare da dama daga cikin shugabannin jam’iyyar sa wadanda jami’an tsaro su ka zarga da shirya rikici.
‘Yan sanda sun bayyana cewa zirga-zirgar ababen hawa ta koma dai-dai a Islamabad, amma magoya bayan Mista Khan na zanga-zanga a wasu biranen.
Wani hoto ya bayyana dauke da yadda aka bankawa gidan Rediyon Peshawar wuta a ranar Laraba.
An kara yawan sojoji a yankunan kasar don kare rikidewar zanga-zangar zuwa rikici.