Ban Gama Bayyana Rayuwar da Kasar Hausa ke Ciki ba Har Yanzu a Film din “MANYA MATA” – Abdul Amart

Hannatu Suleiman Abba

Abdulrahman muhammad Wanda aka fi sani da Abdul Amart ya ce har yanzu Bai Gama fayyace abubuwa da Shirin Nan me dogo zango ya kusa game da rayuwar da ake ciki a kasar Hausa.

Abdul Amart Wanda shine ya shirya Shirin MANYA MATA ya kara dace wa ,babu wata kungiyar ko Hukumar da ta dau nauyi Shirin illa son da kishi al’umma da ya saka a gaba wajen Ganin al’umma sun gyaru.

“Idan mukace muna koyar da tarbiyya sai ayi chaa akan mu. Shirin Manya Mata ya tabo kowanne fanni na rayuwa da al’umma hausawa ta tsinci kanta a wanna zamani” a cewar sa.

MANYA MATA Shirin ne da ya Shiga cikin al’umma wajen yi bincike tare da kawo gyara, baya nuna rashin kunya ko Kuma Bata tarbiyya ko fito na fito da maza, duk da mun nuna Mata masu gwagwarmaya a sahu gaba.

Haka na da Nasaba akan yadda sunfi maza kafa kungiyoyi kwato hakki Mata da kananan Yara hakkin su tare da taimako a kasar Hausa,Inji Amart

Da dama a kasar Hausa a Yanzu, idan na miji ya aura mace, Kai tsaye zai ga alfarma yayi Mata, Bai damu da ci ko Sha din ta ba, wulakanci da cin zarafi sunfi yawa.

Akwai matar da muka samu labari ta sai ta siyar da mutunci ta ,kafin zata samu abinci da zata ci da Ya’yan ta.

Hakazalika, Shirin MANYA MATA bazai tsaya ana ba, Za mu nuna amfani ilimi addini ta bangare karatun almajiranci ,domin akwai iyayen da suke Kai Ya’yan su da abinci da zasu ci, idan zasu Kai su makarantar almajiranci. domin shima malamin Yana da nasa iyalan.

A dai cikin Shirin MANYA MATA ,zamu Kara haska halin da kasar mu ke ciki, wato yadda cin hanci da rashawa ya addabi kasar mu,rufe boda, rashin tsaro da sauransu.

Babban buri na game da Shirin MANYA MATA shine, al’umma su gyaru ,duk da Ina samu Kira a duk fadin duniya aka cewa ,an Dade ba’ayi Shirin da ya nuna halin da kasar hausa ke ciki ba kamar wanna. Sanna Shirin MANYA MATA Babu Wanda ya dau sa, zuba kudi mukayi domin mu kawo sauyi a cikin rayuwa mu, Ba muyi Shirin don samu kudi ba. Kofar mu a bude take ga wayenda suke son daukar nauyi Shirin yanzu ,bada shawara da Kuma gudumawa.

Shirin MANYA MATA zai dawo a Karo na biyu a watan yuli a wannan shekarar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here