Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Legas ta Kama Waɗanda Suka Kona Mawaki Akan N100
Rundunar ‘yan sanda ta kame wasu mutum hudu da ake zargi da kashe wani mawaki a jihar Legas tare da kone shi.
Wannan lamari ya faru ne yayin da rikici ya barke tsakanin abokan wanda aka kashen da wasu ‘yan acaba.
Wannan lamari ya haifar da tada kura a kafafen sada zumunta, inda wasu suke nemawa mawakin adalci.
jihar Legas – ‘Yan sanda a jihar Legas sun kama wasu mutane hudu da ake zargin sun yi wa wani David Imoh mai shekaru 38 kisan gilla ta hanyar kone shi a yankin Lekki Phase One na jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, kama mutanan a ranar Lahadi.
A cewarsa:
Read Also:
“Al’amarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Mayu, 2022. An kama mutane hudu a ranar game da wannan aika aika. Muna kan hanyar kama mutum na biyar, yanzu muna nemansa.
“Wanda aka kashe shine David Imoh, mai shekara 38. Za a gurfanar da wadanda ake zargin idan an kama su. Za mu tabbatar an gurfanar da su gaba daya domin su zama darasi ga wasu.”
A cewar Mista Hundeyin, wanda Sufeto na ‘yan sanda ne, ba a yarda da daukar doka a hannu a jihar Legas ba, ya kuma gargadi jama’a da su guji irin haka.
Ya kara da cewa:
“Kada ku dauki doka a hannunku.”
A baya NAN ta tattaro cewa wasu da ake zargin ‘yan acaba ne da ke aiki a yankin Lekki Phase One sun lakada wa David dukan tsiya a kan rikicin da ya barke kan N100.
An ce, duk da bayanin da Philip ya yiwa ‘yan acaban, sun dage cewa dan Yahoo ne wanda har ta kai suka cinna ma David wuta, inji rahoton This Day.
An samu cewa rashin jituwar ta haifar da hargitsi tsakanin David da daya daga cikin ‘yan acaban.