‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da ɗan Majalisar Jahar Anambra

Wasu miyagun yan bindiga sun sace ɗan majalisar jiha mai wakiltar Aguata 1 a majalisar dokokin jihar Anambra, sun bar motarsa.

Kakakin hukumar yan sanda na jihar, Mista Ikenga, ya tabbatar da lamarin, ya ce jami’an sun bazama neman kubutar da shi.

Ya kuma musanta labarin da mutane ke yaɗawa cewa wani ɗan Bijilanti da aka gano gawarsa ɗan sanda ne.

Anambra – Hukumar yan sanda ta jihar Anambra ta tabbatar da sace, Okechukwu Okoye, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Aguata 1 a majalisar dokokin jihar Anambra.

Honorabul Okoye, wanda ɗan asalin garin Isoufia ne inda gwamnan Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya fito, ya shiga hanun masu garkuwa ne a garin Aguata ranar Lahadi.

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN).

Premium Times ta ruwaito cewa an gano motar da ɗan majalisar ke ciki yayin da lamarin ya faru Siena SUV, a cewar hukumar yan sanda.

Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?

Kakakin yan sandan, Mista Ikenga, ya ce tuni jami’an yan sanda suka bazama neman masu garkuwan da kuma kubutar da ɗan majalisar cikin koshin lafiya.

Haka nan kuma ya tabbatar da kashe mamban ƙungiyar yan Bijilanti, wanda ke kan Babur a garin Oko, jihar Anambra duk a ranar Lahadi.

Ikenga ya ƙara da cewa ɗan Bijilantin da aka kashe na sanye kayan jami’an tsaro na musamman, amma ba jami’in hukumar yan sanda ba ne.

Ya kuma ƙaryata rahoton da mutane ke yaɗa wa a kafafen sada zumunta cewa mamacin ɗan sanda ne, inda ya roki al’umma su yi watsi da rahoton.

Ya ce:

“A ranar 15 ga watan Mayu, jami’an hukumar yan sandan jihar Anambra sun gano wata gawa sanye da rigar yan sanda a kan babbar hanyar Oko, kuma bincike ya nuna ba mamba bane a hukumar yan sanda.”

“Hukumar yan sanda ta fara bincike don gano ainihin bayanan mamacin tare da gano musabbabin da ya haddasa mutuwarsa.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here