Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Oyo Sun Kama ‘Dan Shekara 16 Mai Satar Shanu

 

Rundunar ‘yan sanda a jahar Oyo sun cafke wani matashi dake aikin satar shanu da garkuwa da mutane.

Matashin ya bayyana yadda ya shiga harkar tare da bayyana wadanda suka nuna masa mummunar sana’ar.

A halin yanzu an kama shi tare da wani abokin harkallarsa yayin da aka kuma gabatar dasu ga manema labarai.

Rundunar ‘yan sandan jahar Oyo ta cafke wani barawon shanu mai shekaru 16, Umaru Muhammed, kan garkuwa da mutane a Ibadan.

Muhammad ya amsa cewa yana cikin gungun masu garkuwa da mutane yayin da yake amsa tambayoyi a hedkwatar rundunar, Eleyele, Ibadan, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa,wanda suka yi awon gaba dashi na karshe sun rude shi da ya zo ya sayi shanu ne a kauyen Akinyele, Karamar Hukumar Akinyele a Ibadan, babban birnin jahar Oyo.

Wanda ake zargin da ya amsa cewa shi barawon shanu ne ya ce wasu abokan aikinsa da a yanzu suke nemansa sun ce ya kira mutane su zo su sayi shanu a wurinsa.

Dangane da yadda ya sami damar gudanar da aikin, wanda ake zargin ya ce: “An nemi in kira kwastomomi na su zo su sayi shanu. Sannan, na kira Taofeek kuma ya zo ya same ni a kauyen mu.

Amma a kan hanyarmu ta zuwa wani kauye, mutanena suka kawo mana hari.

“Mun tsara mu sace su don neman kudin fansa amma abin takaici wasu matasan kauye suka dakile shirin. An kawo karshen shirin harbe-harbe kuma an kashe daya daga cikin matasan kauyen a cikin farmakin.”

Ban taba garkuwa da mutane ba A cewarsa, bai taba garkuwa da mutane ba a baya amma mutanensa kan yi hakan sau da yawa, wanda da yawa daga cikinsu ya ce sun gudu.

Ya kara da cewa:

“Sun gayyace ni in shiga aiki tare da su kuma sun ba ni dabarar da zan yi amfani da ita.

Sun yi min barazanar cewa idan ban ba su hadin kai ba, za su yi magani na kuma sun tilasta ni in yi abinda suka umarce ni.

“Daya daga cikin mutanena da muka shirya aikin tare an kama shi nan take kuma kama shi ne ya kai ga kama ni.”

Da yake gabatar da wadanda ake zargin gaban manema labarai, Kwamishinan ‘yan sandan jahar, CP Ngozi Onadeko, ya bayyana sunayen wadanda ake zargin a matsayin Usman Mohammed mai shekaru 27, da Umaru Mohammed mai shekaru 16.

Ngozi ta ce a ranar 9 ga Yuli, 2021, wani Taofeek Olaide ya sami kiran waya daga wani mutum Umaru Mohammed, yana mai cewa yana da shanu don sayarwa bisa umarnin mahaifinsa a kasuwar Kara, yankin Akinyele a Ibadan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here