Mun Kama Mutane 6 Kan Batan ‘Dan Jarida – Rundunar ‘Yan Sanda Najeriya
Rundunar yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum shida bayan batan dan jaridan nan na Vanguard Tordue Salem.
Kusan mako biyu kenan da dan jaridar ya yi batan dabo a Abuja, babban birnin kasar.
Read Also:
Ranar Litinin yan jarida karkashin kungiyar NUJ sun gudanar da zanga-zanga a hedikwatar ‘yan sanda a Abuja, kan abin da suka kira ‘nuna rashin damuwa’ kan batan abokin aikinsu.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Najeriya Frank Mba, ya bai wa yan jaridar tabbacin yin duk iya yinsu wurin gano inda dan jaridar yake.
Kuma ya ce sun cafke mutum shida kan batun yayin da ake ci gaba da bincike,
Kafin batan Tordue Salem shi ke dauko wa jaridar Vanguard rahotanni daga majalisar dokoki, kuma rabon da a sa shi a ido, ko a ji daga gare shi tun ranar 13 ga watan Oktoba.