Taron Zuba Jari :Shugaba Buhari ya Isa Saudiyya 

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa birnin Riyadh na Saudiyya, inda zai halarci taron zuba jari na Future Investment Initiative Institute.

Mataimaki na musamman ga Shugaban kan yada labarai Malam Garba Shehu, ya sanar cewa Shugaba Buhari ya sauka birnin da misalin karfe 11:50 na dare ranar Litinin.

Garba Shehu ya kara da cewa “Shugaban zai halarci bikin kaddamar da taron zuba jarin na kwanaki uku da da za a fara yau Talata, wanda zai mayar da hankali kan zuba jari don inganta rayuwar al’umma.”

Ana sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai gudanar da aikin Umra kafin dawowa Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here