Jahar Kano ta Kama Mutane Sama da 200 da Laifin Saba Dokokin Hana Yaɗuwar Cutar Corona

 

Kwamitin da ke kula da cutar corona a jahar Kano ya kama mutum sama da 200 a kokarinsa na tabbatar da bin dokokin hana yaɗuwar annobar kamaa jahar.

Daga cikin mutane 200 da aka kama an tura 25 gidan gyara hali.

Shugaban kwamitin ya tabbatar da cewa an samu mutum 102 da laifin saba doka kuma sai da aka ci tarar ko wannensu N5,000.

Rahotanni sun nuna cewa kotun da ke hukunta wadanda suka karya dokar korona a jihar Kano, ta tura mutane 25 gidan gyara hali bayan ta kama su da laifi.

An tattaro cewa akalla mutane 200 jami’an tsaro suka tsare sakamakon karya dokar korona da gwamnatin jahar ta shimfida wanda daga cikinsu aka ci tarar wasu.

Shugaban hukumar Karota, Baffa Babba DanAgundi, ya ce: “Mun gode Allah da mutanen Kano ke bin dokar sanya takunkumin fuska domin kare lafiyarsu.

“Duk marasa bin doka da ke kin sanya takunkumin fuska za su hadu da fushin hukuma.Saboda haka dokar kariyar korona ta zauna ke nan.”

Bayan fara aiki da dokar sanya takunkumi, Gwamnatin Kano ta kafa kotun tafi-da-gidanka kimanin guda 21, wanda DanAgundi ke jagoranta.

Ya bayyan cewa an kama masu karya dokar har mutane 102 da aka ci tarar kowanensu N5,000.

Ya kara jan hankalin shugabanin kasuwanni da tabbatar da bin dokar kare kai daga annobar.

Da yake jawabi, Kwamishinan Yada Labaran jahar, Muhammad Garba ya ce sabuwar dokar za ta tabbatar da kare mutane daga kamuwa da cutar korona.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jahar ta dauki matakin ne saboda yadda cutar ke kara yaduwa a jahar tun bayan sake bullarta a karo na biyu, jaridar Aminiya ta ruwaito.

Ya ce duk wanda kotun tafi-da-gidanka ta samu ya karya dokar to za a hukunta shi yadda doka ta tanada don haka ya ja hankalin jama’ar jahar da su kasance masu bin doka a kodayaushe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here