Kama Sojoji 7 Masu Alaƙa da ‘Yan Fashi: Rundunar ‘Yan Sandan Zamfara ta ƙaryata Rahotannin
Rundunar ƴan sandan jahar Zamfara ta ƙaryata rahotannin da ke cewa ta kama wasu jami’an sojoji guda bakwai da ake zargi suna da alaƙa da ayyukan ƴan fashi a jahar.
Sanarwar da kakakin ƴan sandan Zamfara SP Mohammed Shehu ya tura wa manema labarai ta ce babu wani soja da ƴan sanda suka kama saɓanin yadda ake yaɗawa a kafofin sada zumunta na intanet.
Sanarwar ta ce labarin ƙarya ne ake yaɗawa tare da yin gargaɗi ga masu yaɗa labaran ƙarya cewa duk wanda aka kama zai fuskanci fushin hukuma.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here