Dakarun Sojojin Najeriya Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3 a Jahar Enugu
Dakarun sojojin Najeriya sun ce sun kashe ƴan bindiga uku a Jahar Enugu da ke kudancin ƙasar.
Wata sanarwa daga kakakin rundunar, Onyema Nwachukwu, ta ce sun kashe ƴan bindigar ne waɗanda suka kai wa ƴan sanda hari ranar Alhamis a wani shingen binciken jami’an tsaro kan babbar hanyar Okija-Onitsha a ranar Alhamis.
Ya ce ɓangaren dakarun rundunar Golden Dawn da aka tura Enugu sun murƙushe ƴan bindigar a musayar wuta, wanda ya tursasa masu tserewa.
“Yan bindiga uku aka kashe, waɗanda ke cikin mota biyu ƙirar Hilux da Hummer, yayin da wasu suka tsere da harbin bindiga a jikinsu.”
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here