Mutane da Dama Sun Rasa Rayakansu Sanadiyyar Hatsarin Jirgin Ruwu a Kongo

 

An tabbatar da mutuwa ko ɓacewar mutum fiye da 100 bayan wani jirgin ruwa ya kife da su a Kogin Kongo, kamar yadda hukumomi a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo suka bayyana ranar Asabar.

An ɗebo gawar mutum 51 ya zuwa Juma’a da dare bayan hatsarin ya faru a daren Litinin zuwa Talata. Kazalika ana zaton wasu 69 sun ɓace.

Gwamnan yankin Mongala, Nestor Magbado, ya faɗa wa AFP cewa mutum 39 sun tsira daga hatsarin.

A cewarsa, tun da yake babu rajistar fasinjojin da ke cikinsa, an ƙiyasta adadin waɗanda suka ɓace ne ta hanyar lura da adadin da jirgin zai iya ɗauka.

Ya alaƙanta hatsarin da “lodin wuce kima da kuma rashin kyawun yanayi” a matsayin abubuwan da suka haddasa shi.

latest naija news now

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here