Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Zamfara ta Bayyana Yadda ta Kama ‘Yan Bindiga 21 a Jahar

 

A ranar Lahadi, rundunar ‘yan sandan jahar Zamfara ta bayyana yadda ta kama ‘yan bindiga 21 a jahar.

Har ila yau, ta kama masu taimaka mu su guda 69 sakamakon sintiri da binciken da su ka yi a watan Satumba .

Jami’in hulda da jama’an rundunar, SP Muhammad Shehu ne bayyana hakan ga manema labarai a Gusau.

Zamfara – A ranar Lahadi, rundunar ‘yan sandan jahar Zamfara ta bayyana yadda ta samu nasarar kama mutane 21 da ake zargin ‘yan bindiga ne da su ka addabi jahar tare da masu taimaka musu guda 69 duk a cikin watan Satumba.

SP Muhammed Shehu, jami’in hulda da jama’an hukumar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau, inda yake lissafo tarin nasarorin da jami’an tsaro su ka samu a jahar.

Shehu ya ce sun halaka manyan ‘yan bindiga 5

Kamar yadda ya bayyana, sun halaka shu’uman ‘yan bindiga 5 da jami’an tsaro su ka bayyana su na nema ido rufe.

Kamar yadda Vanguard ta rawaito, ya bayyana cewa:

“Tun bayan gwamna Bello Matawalle na jahar Zamfara ya samar da sababin dabarun kawo karshen rashin tsaro a jahar, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun cigaba da bin hanyoyin kawo karshen ‘yan bindiga da sauran miyagun mutane dake jahar.

“Sakamakon yadda jami’an tsaro su ka jajirce kuma su ka dage, an samu nasarori da dama don yanzu haka an halaka ‘yan bindiga sannan kuma hari, kashe-kashe da garkuwa da mutane duk sun rage a watan da ya gabata.

“Hanyoyin da gwamnan ya samar sun dakatar da ‘yan bindiga daga samun abinci, man fetur, magunguna har da sauran ababen bukatun su.

“Yanzu haka an dakata daga biyan su kudaden fansa duk sakamakon tsaron da gwamnan ya sa a jahar, yanzu haka babu hanyar sadarwa tsakanin ‘yan bindiga da masu ba su bayanai na musamman.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here