Hukumar Alhazai ta Birnin Tarayya ta Sanar da Ranar Kammala Biyan Kuɗin Hajjin 2023

 

Hukumar jindaɗin Alhazai ta birnin tarayya Abuja ta bayyana ranar kammala biyan kuɗin Hajjin bana.

Hukumar tace saɓawa hakan ka iya janyowa maniyyata matsala wajen tafiya zuwa ƙasa mai tsarki.

A cewar hukumar maniyyatan da suka kammala biyan kuɗinsu akan kari suna da wata garaɓasa ta daban.

Abuja- Hukumar jindaɗin Alhazai ta birnin tarayya Abuja, ta bayyana cewa maniyyatan bana na birnin tarayya Abuja da suka fara biyan kuɗin Hajjinsu, suna da daga nan zuwa ranar 21 ga watan Afrilu domin kammala biyan kuɗin.

NAHCON a ranar Juma’a ta sanar da cewa maniyyatan bana daga birnin tarayya Abuja za su biya N2,919,000 a matsayin kuɗin Hajjin bana, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Wata sanarwa daga kakakin hukumar Muhammad Lawal Aliyu, ta bayyana cewa wa’adin an sanya shi ne domin ba hukumar damar cika wa’adin da NAHCON ta sanya dukkanin jihohi da birnin tarayya domin kammala biyan kuɗin aikin Hajjin bana.

Sanarwar tayi bayanin cewa cikata ragowar kuɗin zai ba hukumar damar kammala haɗa jerin sunayen maniyyatan bana, duba da cewa lokacin fara jigilar maniyyatan zuwa ƙasa mai tsarki na ƙara ƙaratowa.

Ya bayyana cewa biyan cikon kuɗin zai sanya hukumar ta cigaba da sauran shirye-shiryen tafiya da kuma cika umurnin wa’adin da NAHCON ta sanya domin kammala biyan kuɗin hajjin bana.

Kakakin ya kuma jaddada cewa waɗanda kawai suka kammala biyan kuɗin zuwa ranar wa’adin ne, za a sanya sunayensu a cikin jerin sunayen maniyyatan bana.

Akwai garaɓasa ga waɗanda suka kammala biyan kuɗin su

Ya kuma ƙara da cewa bayan maniyyatan sun kammala biyan kuɗinsu, za a ba su damar zaɓar jirgin da suke son ya kai su ƙasa mai tsarki lokacin jigila, rahoton jaridar Independent Yayi bayanin cewa za a cigaba da wayar da kan maniyyata a ranakun 29 da 30 na watan Afirilu, a sansanin Alhazai na dindindin da ke a Bassan Jiwa kusa da tashar filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here