Duk Wanda ya Kamo Ado Aleru Zai Samu kyautar N5m – Rundunar ‘Yan Sanda

Duk wanda ya kamo ko ya bayar da bayani kan inda shugaban yan bindiga, Ado Aleru, yake zai samu kyautar naira miliyan 5.

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta ayyana neman Aleru ruwa a jallo kan zarginsa da kashe sama da mutum 100.

A ranar Asabar ne dai Sarkin Yandoton Daji, Aliyu Marafa, ya nada gogarmar dan ta’addan sarautar Sarkin Fulani.

Katsina – Rundunar yan sandan jihar Katsina ta ayyana neman gogarmar dan bindiga, Ado Aleru, wanda Sarkin Yandoto na Zamfara ya nadawa sarautar Sarkin Fulani a ranar Asabar ruwa a jallo.

Ana neman Aleiro ne kan zargin aikata ayyukan ta’addanci ciki harda kashe akalla mutane 100, jaridar Vanguard ta rahoto.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin Yandoton Daji, Aliyu Marafa, kan nadawa dan ta’addan da ake nema ruwa jallo sarauta.

Kakakin yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa, ya ce duk wanda ya kama ko ya bayar da bayanan da za su kai ga kama gogarmar dan bindigar, zai samu kyautar naira miliyan 5, yana mai cewa dan ta’addan ya kashe fiye da mutane 100 a jihar Katsina ciki harda mata da yara, Channels TV ta rahoto.

Ya kuma bayyana cewa Aleiro na cikin yan bindigar da rundunar ke nema saboda ya kashe tare da sace mutane da dama.

A cewarsa:

“Muna neman Aleru ne saboda ayyukan ta’addanci da ya aikata a garin Kadiso inda ya kashe mazauna kauyen fiye da 100. Mun kasance tare da kwamishinan yan sanda, Sanusi Buba da yan jarida a Kadiso inda muka ga yadda ya kashe mutane ciki harda mata da yara, da kuma lalata kayayyakin abinci da dabbobi.

“Hakan ne ya sa rundunar ‘yan sandan Katsina ta fitar da sanarwar cewa duk wanda ya kama Aleiro ko a mace ko a raye za a ba shi naira miliyan 5. Wannan al’amari yana nan. Muna nemansa kuma duk wanda ya ganshi ya kawo mana rahoto. Muna tuhumar sa da aikata ta’addanci a Kadiso, da sauran garuruwa ma. Ya kuma yi garkuwa da mutane sannan ya karbi kudin fansa.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here