‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Basarake a Abuja

Wasu yan bindiga dauke da makamai sun sace mai unguwar Kuchibiyu da ke Kubwa, ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin Najeriya Abuja.

Wata majiya a unguwar ta ce an sace Malam Isiaka Dauda ne a cikin gidansa, mitoci kaɗan zuwa fadarsa, lokacin harin wanda aka fara kai wa tun daga sha biyu na dare zuwa daya na dare.

Ya ce ƴan bidigar da yawansu ya kai goma, sun yi harbi sau biyu bayan zuwansu, abun da ya jfa fargaba a zukatan mutan.

Ya ƙara da cewa da farko maharan sun danna wani ɗaki ne da suka samu basaraken a ciki.

‘’Sun tafi da shi ba tare da tirjiya ba, ta wata hanya marar kyau suka bi suka ɓulle suka tafi’.

Har kawo yanzu dai masu garkuwar ba su buƙaci komai ba tukuna.

Babban jami’in ƴan sandan yankin Kubwa ACP Muhammad Ndagi wanda ya tabbatar da aika-aikar ya ce za su yi bincike a kan al’amarin.

Wannan na faruwa ne watanni uku bayan yin garkuwa da mai unguwar Bukle da ke yankin Kwali a Abujan Alhaji Hassan Shamisozhi a fadar shi.

An sake shi bayan shafe kwanaki goma sha takwas a hannun masu garkuwar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here