Jihar Kano na Bukatar Allura Miliyan 6 Don Magance Cutar Mashaƙo – Gwamna Abba
Gwamna Abba Gida Gida na jihar Kano, ya bayyana adadin allurar rigakafin cutar Mashaƙo da suke buƙata.
Ya ce aƙalla suna buƙatar allurar rigakafi miliyan shida domin yaƙi da cutar mashaƙo ta ‘Diptheria’ a jihar.
Ya bayyana hakan ne a yayin da ya karɓi baƙuncin gidauniyar Bill & Melinda Gates Foundation.
Kano – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana adadin allurar rigakafin da suke buƙata domin magance cutar mashaƙo ta ‘diptheria’ da ta addabi jihar.
Read Also:
Ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi wakilan gidauniyar Bill & Melinda Gates Foundation a gidan gwamnatin jihar.
Jihar Kano na bukatar allura miliyan 6 don magance Mashaƙo
Abba wanda mataimakinsa Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta, ya bayyana cewa jihar Kano na buƙatar aƙalla allurar rigakafi miliyan 6 domin magance cutar mashaƙo da ta addabi jihar.
Ya jaddada aniyar Gwamnatin jihar na ganin ta ƙara ƙarfafa haɗakar da ke tsakanin gwamnatin jihar Kano da gidauniyar ta Bill & Melinda Gates Foundation kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnatin Kano a kwanakin baya, ta ƙaddamar da wasu cibiyoyi guda uku a faɗin jihar da za a riƙa kwantar da waɗanda suka kamu da cutar ta Mashaƙo kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.