Gwamnatin Kano na Kashe N4bn Kowacce Shekara Don Ciyar da ‘Yan Makaranta

Gwamnatin jihar Kano wacce Ganduje ke jagoranta ta ce tana kashe naira biliyan 4 duk shekara wurin ciyar da ‘yan makarantun kwana.

Kwamishinan ilimi, Sunusi Kiru ya sanar da hakan ranar Talata a wata hira da yayi da manema labarai a kan nasarorin gwamnatin.

Ya ce yanzu haka ana nan ana karasa ginin makarantu 5 a masarautu 5 da ke jihar, Masarautar Kano, Gaya, Karaye, Rano da Bichi Gwamnatin jihar Kano wacce Gwamna Abdullahi Ganduje yake jagoranta ta ce tana kashe naira biliyan 4 duk shekara wurin ciyar da daliban makarantar kwana da ke jihar.

Kwamishinan ilimi, Sunusi Kiru, ya sanar da hakan ga manema labarai a kan nasarorin da ma’aikatar ta samu cikin watanni 12, Channel TV ta wallafa. Ya ce gwamnatin Ganduje ta fi bayar da muhimmanci ga ilimi, musamman yadda yasa shi ya zama kyauta kuma tilas a kan kowa.

Kwamishinan ya bayyana ginin makarantu 5 a masarautar Kano, Gaya, Karaye, Rano da Bichi sun kusa kammaluwa. Ana sa ran komawa makarantu daga watan Janairun 2021, tare da sababbin dalibai 360 a kowacce makaranta.

“Gwamnatin jihar ta samar da wata babbar makarantar sakandare ta fasaha da ke garin Ganduje, a karamar hukumar Dawakin Tofa.

“Yanzu haka ana cigaba da karasa ginin katangu, azuzuwa 6, mota mai daukar mutane 32 da wata motar kirar Hilux don zirga-zirgar makarantar,” cewar Kiru.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here