Najeriya: Shugaban Kasar na Jagorantar Zaman Majalisar Zartarwa
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar zartarwa ta kasa.
Taron na gudana ne a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa a yau Laraba, 4 ga watan Nuwamba.
Mataimakin shugaban kasa, wasu manyan gwamnati da ministoci bakwai sun hallara yayinda sauran suka shiga taron ta yanar gizo daga ofishoshinsu Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar zaman majalisar zartarwa ta yanar gizo karo na 22, a yau Laraba, 4 ga watan Nuwamba, a fadar Shugaban kasa, Abuja.
Read Also:
Taron wanda ke gudana a zauren majalisar da ke fadar Shugaban kasa, ya samu halartan mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.
Ministoci bakwai da suka hallara sun hada da Ministan Shari’a, Abubakar Malami; Ministan Birnin Tarayya, Muhammad Musa Bello; Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; da Ministan Bunkasa Wasanni da Harkokin Matasa, Sunday Dare.
Sauran sune Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da kuma Ministar Kudi, Zainab Ahmed. Shugabar ma’aikatan tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan da sauran ministoci sun halarci taron ne ta yanar gizo daga ofishoshinsu mabanbanta a Abuja.
Taron na gudana ne a a daidai lokacin da wa’adin mako guda da Buhari ya ba wa ministoci kowannensu ya kawo rahoton ganawarsa da jama’ar jiharsa ke cika.