Kaduna: ‘Yan bindiga Sun Kashe Mata Mai Juna Biyu Sunyi Garkuwa da Mijinta

‘Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun afka gida sun sace mata mai juna biyu da mijinta a Kaduna.

Matar mai juna biyu ta mutu sakamakon harbinta da ‘yan bindigan suka yi yayin musayar wuta da ‘yan sanda.

‘Yan bindigan sun yi nasarar yin awon gaba da mijin matar da suka sace yayin da ita kuma matar anyi mata jana’iza An ruwaito cewa wasu da ake zargin masu garkuwa ne sun kashe wata mata mai juna biyu a Kaduna a ranar Talata a unguwar Rigachikun.

Wata majiya ta shaida wa The Nation cewa ƴan bindigan sun sace matar ne tare da mijinta daga gidansu. Majiyar ta ce wadanda ake zargi masu garkuwar ne sun kashe matar yayin da suke musayar wuta da jami’an tsaro da ke ƙoƙarin ceto wadanda abin ya faru da su.

Har yanzu ba a gama samun cikakken bayani kan afkuwar lamarin ba.

Kakakin rundunar ƴan sandan Kaduna, ASP Muhammad Jalige bai riga ya amsa tambayar da aka masa game da lamarin ba.

Amma majiyar ta ce, “Masu garkuwar sun afka gidan wadanda abin ya faru da su suka yi awon gaba da su, daga nan jami’an tsaro suka bi sahun su inda yayin musayar wuta masu garkuwar suka harbe matar kuma daga bisani ta mutu a asibiti.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here