Kano Pillars ta Sayi Sabbin ‘Yan Wasa
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta ƙaddamar da sabbin ‘yan wasa tara da ta saya domin fara kakar wasa ta 2020-21 a gasar Firimiyar Najeriya ta Nigeria Professional Football League (NPFL).
‘Yan wasan sun haɗa da tsohon ɗan wasan ƙungiyar Niger Tornadoes, Mustafa Jibrin, da Jeremie Heutchou daga Apejas ta Afirka ta Kudu, da Munkaila Musa daga ƙungiyar Yobe Desert Stars, da Ayobami Juniors daga Shooting Stars.
Read Also:
Sauran su ne Frank Guiman daga AS Tonere ta ƙasar Benin, da Nnaji David daga El-Kanemi Warriors, da Manji Williams daga Wiki Tourists, da Haruna Sule daga Adamawa United, da Ogujigba Ezekiel daga Lobi Stars.
Kazalika, an gabatar da sabon koci farar fata ɗan ƙasar Faransa mai suna Lione Emmanuel Soccia da ƙungiyar ta ɗauka a farkon makon nan.
Da yake ƙaddamar da ‘yan wasan a Kano, shugaban ƙungiyar Surajo Shuaibu ya faɗa wa manema labarai cewa sabbin ‘yan wasan za su maye gurbin waɗanda kulob ɗin ya sallama ne a ƙarshen kakar 2019-20.