Kano: Hadimin Gwamnan ya Rabawa Matasa Jakuna
An saka jaki ne saboda daya daga cikin wanda zasu amfana da tallafin ya bukaci hakan.
An raba wasu kayayyaki da dama kamar babura da kwanukan rufi da bulon gini.
Jiga jigan ma’aikatar matasa sun halarci taron da ya gudana a harabar ma’aikatar a ranar Alhamis.
Mataimaki na musamman ga gwamna Ganduje akan harkokin ci gaban matasa, Murtala Gwarmai a ranar Alhamis 12 ga watan Nuwamba ya rabawa matasa jakuna da sauran kayayyaki don tallafa musu.
Read Also:
The Cable ta ruwaito cewa matasan da ba su gaza arba’in ba a fadin jihar ne suka amfana a taron da ya gudana a harabar ma’aikatar matasa da wasanni.
Gwarmai ya kuma raba babura, kudade kimanin 100,000, bulon gini da kuma kwanon rufi da ma wasu da dama, yace dalilin da yasa aka saka jaki shine, daya daga cikin wanda za su amfana da tallafin ne ya bukaci a bashi saboda yana amfani dashi wajen safarar yashi, dutse da bulo, kuma yace zai taimaka masa wajen bunkasa kasuwancin sa.
Wanda suka halarci taron sun hada da kwamishinan matasa da wasanni, Kabiru Ado Lakwaya, babban mai bada shawara kan harkokin matasa II Ibrahim Ahmad da sauran jiga jigan ma’aikatar.