Hatsarin kwale – Kwale: Wasu Mutane sun Rasa Rayukansu a Jahar Bauchi

Kwale-kwale ya kife da mutane 23 inda 18 suka rasa rayukansu a Bauchi.

Daga cikin wanda hatsarin ya afkawa akwai yara yan shekara 16 zuwa 18.

An ceto matukin da wasu mutane 4 cikin mawuyacin hali inda aka garzaya dasu asibiti.

Bala’i ya afku a jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma’a 13 ga watan Nuwamba.

Daga cikin wanda suka rasu akwai yara tsakanin shekara 18 da 16.

Wanda hatsarin ya rutsa da su an dauko su ne daga kauyen Zango Majiya a karamar hukumar Itas Gadau zuwa gonakinsu lokacin da kwale-kwalen ya kife kuma suka nutse a tsakiyar Kogin Buji.

Kakakin yan sandan ya ce an ceto mutane biyar cikin su harda matukin cikin mawuyacin hali sannan an garzaya da gawawakin zuwa babban asibitin Itas don gudanar da bincike.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here