Jos: An Samu Barkewar Gobara a Ofishin Hukumar Wutar Lantarki

Hedkwatar hukumar samar da wutar lantarki na Jos da ke kan titin Ahmadu Bello Way, Jos, ta kama da wuta a ranar Juma’a.

Sakamakon gobarar, sassa da dama na garin na zaune cikin duhu. An gano cewa wutar ta fara ne daga hawa na hudu na ginin misalin karfe 6 na yamma.

Shugaban sashin hulda da jama’a na kamfanin, Dakta Adakole Elijah ya tabbatar da faruwar lamarin a wayar tarho da suka yi da The Punch.

Elijah ya ce, “Eh, da gaske ne. Babban ofishin mu na Jos ya yi gobara amma an sanar da jami’an hukumar kwana kwana na Jos kuma suna kokarin kashe wutar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here