Mai Shariah na Babbar kotun jihar Kano AT Badamasi ya sanya ranar sha hudu ga watan Janairu domin yanke hukunci kan dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf.

Tun da farko dai Jafar Sani Bello Wanda shi ne yazo na biyu a zaben da ‘Yan Kwankwasiyya suka yi na fitar da dan takarar Gwamnan Kano a jam’iyyar PDP ya shigar da kara inda yake bayyana kotu cewar Abba Kabir wanda aka ce shi ne ya zama dan takara bai cika ka’idar shigowa PDP ba.

Jafar Sani Bello ya shaidawa kotu cewar a bisa tanadi na kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP Abba bai shaidawa mazabarsa a rubuce cewar ya dawo jam’iyyar ba, wanda dole Sai yayi haka sannan ya zama cikakken dan jam’iyya.

Nan da sha Hudu ga watan Janairu ne dai Abba Kabiru Yusuf da Jafar Sani Bello zasu san matsayarsu akan wannan shariah.

The post Kano: Takarar Abba Kabir Yusuf na tangal tangal appeared first on Daily Nigerian Hausa.

latest nigerian breaking news

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here