ƙarancin Naira: Ana Zanga-Zanga a Sassan Jihohin Najeriya
Tarzoma ta ɓarke a wasu sassan jihar Lagos da safiyar yau Juma’a inda wasu da ake zargin ɓata-gari ne suka bazama manyan ttituna suna zanga-zanga a kan ƙarancin takardun kuɗin ƙasar na naira.
Jaridar Vanguard wadda tana daga cikin jaridun ƙasar da suka ruwaito, labarin masu zanga-zangar sun yi cincirundo a unguwannin Mile-12 da Ketu da Ojota, a kan titin Ikorodu, Iyana-Ipaja da misalin ƙarfe shida na safe, kafin ta fantsama zuwa wasu yankunan kamar Agege da Iyana-Iba.
Read Also:
Masu motoci da ke kan hanyarsu ta zuwa aiki sun riƙa juyawa a firgice saboda masu zanga-zangar sun rika kunna wa tayoyin da sauran abubuwa wuta suka kashe hanya.
Masu motoci sun tsaya curko-curko a babbar hanyar Lagos/Ibadan sakamakon zanga-zangar.
Tun da farko jaridar ta ruwaito cewa an samu irin wannan tarzoma a jihohin Edo da Oyo da Ogun duka saboda ƙarancin naira da kuma na man fetur.
Ita ma jaridar Punch ta ruwaito cewa ana samun rahotannin irin wannan zanga-zanga a wasu sassan Port Harcourt, babban birnin jihar Ribas.
Rahoton ya ce masu zanga-zngar na cinna wa bankuna wuta