Buhari ya Buƙaci Dukkan ‘Yan Takara da su Mutunta ‘Yancin Masu Zaɓe da Kuma Karɓar Sakamakon Zaɓe da Hukumar Zaɓe za ta Sanar
Shugaba Muhammadu Buhari ya buƙaci dukkan ‘yan takarar kujeru daban-daban a babban zaɓen ƙasar da ke tafe a ranar Asabar da su mutunta ‘yancin masu zaɓe da kuma karɓar sakamakon zaɓen da hannu biyu.
Buhari na magana ne a Abuja jiya Laraba, yayin wani taro da Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa ya shirya domin ganin jam’iyyu da ‘yan takarar kujerar shugaban ƙasa sun sa hannu na yarjejeniyar yin zaɓe lafiya.
Shugaban Najeriyar ya kuma buƙaci wadanda suka ki karɓar sakamakon zaɓen da su bi kadinsu ta hanyar shari’a.
Read Also:
“Ina kira ga dukkan ‘yan takara na kujeru daban-daban a wannan zaɓe da su tabbata sun mutunta ‘yancin masu zaɓe da kuma karɓar sakamakon zaɓe da hukumar zaɓe za ta sanar, wanda sune dka ta bai wa damar yin hakan,” in ji Buhari.
Shugaban ya kuma yaba wa kwamitin zaman lafiya na ƙasa, inda ya ce duk da cewa babu wani taimako na kuɗi da gwamnati ke bai wa kwamitin, ta dai ci gaba da aiki da hukumomi daban-daban domin ganin abubuwa sun tafi daidai da kuma ƙoƙari wajen shiga tsakani kan sha’anin zaɓe.
Shugaba Buhari ya ce yana sane da damuwa da ake nunawa kan yadda za a gudanar da zaɓen da kuma yadda abubuwa za su kasance bayan bayyana sakamakon zaɓen.
Ya ce tun zuwa kan mulki, gwamnatinsa ta yi aiki tukuru wajen tabbatar da ta bar abin tarihi na gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.