Bayan Harbe Shi: An ƙona Gawar ɗan Takarar Sanata na Jam’iyyar Labour a Enugu

 

Wasu mahara sun kashe wani ɗan takarar kujerar Sanata tare da ƙona gawarsa a jiya Laraba lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa yakin neman zaɓe a jihar Enugu da ke kudancin Najeriya.

Mutuwar Oyibo Chukwu na jam’iyyar Labour na zuwa ne da ya rage kwana uku a gudanar da babban zaɓen Najeriya a ranar Asabar – waɗanda ake hasashen za a yi fafatawar da ba a taɓa yi ba a cikin shekaru 24.

An kuma harɓe masu taimaka masa waɗanda suke tare da shi kafin a cinna wa gawarwakinsu tare da motarsu wuta, kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka ruwaito.

“Jam’iyyun siyasa na harin kashe mana mambobi saboda sun ga jam’iyyar mu na ƙara samun goyon baya a jihar kuma suna fargabar cewa za su iya rashin nasara a zaɓukan ranar Asabar,” in ji Chijioke Edeoga, ɗan takarar kujerar gwamna a jihar.

Jam’iyyar ta Labour ba ta ce uffan ba kan harin, sai dai, ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, na kira ga masu zaɓe da su yi zaɓe cikin lafiya da kuma fata mai kyau.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here