A Gaggauta Karbe Makamai da Kwayoyi a Hannun Matasan Fulani Domin Magance Garkuwa da Mutane- Janar Dambazau
Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya) ya yi kira ga cewa a yi gagawan raba matasan Fulani da kwayoyi da makamai.
Dambazau wanda tsohon minista ne na harkokin cikin gida kuma babban hafsan sojojin kasa ya yi wannan kiran ne a wani taro a Abuja.
Tsohon ministan ya jaddada bukatar da ke akwai na daukan matakai domin magance garkuwa da mutane tsakanin matasa fulani a Najeriya.
FCT, Abuja – Tsohon ministan harkokin cikin gida, Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya) ya bukaci a gaggauta karbe makamai da kwayoyi a hannun matasan Fulani a matsayin wani mataki na dakile garkuwa da mutane a kasar.
Dambazau ya yi wannan kiran ne a kasidar da ya gabatar mai taken “Matsalar Makiyaya Fulani” da ya gabatar a taron tsaro na makiyaya fulani a Abuja.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an yi taron ne da nufin gano hanyoyi warware kallubalen da makiyaya fulani ke fuskanta a zamanin nan da nufin samar da tsaro a kasar.
Read Also:
An shirya taron ne da hadin gwiwa da kungiyar Miyetti Allah da Northern Consensus Movement, NCM.
A cewarsa, daya daga cikin matakan da za a dauka shine dakile samun makamai da kwace dukkan makaman da a yanzu ke hannun matasan fulani makiyaya.
Kalamansa:
“Ya kamata mu tsaftace kasar, ina nufin da taimakon NDLEA, ya kamata a yi yaki da shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasan fulani.
“Ya kamata mu tabbatar da adalci da cigaban al’umma da ilimi da lafiyan makiyaya fulani tare da basu damar cigaba a cikin al’umma.
“Don cimma hakan, ya kamata a basu ingantaccen ilimi, lafiya da kuma koyar da su sana’o’i.”
Ya ce wata matsala kuma shine wasu makiyayan da ke zama a daji suna satar mutane don karbar kudin fansa.
Ya kara da cewa:
“A baya ana iya gane makiyayi da sandarsa da ya ke kiwon shanu, a yau da AK-47 da wasu makaman ake ganinsu kuma suna amfani da shi wurin kai wa mutanen kauyuka hari ko garkuwa da fasinjoji a manyan hanyoyi.
“An san makiyayi fulani da saukin kai, tausayi, gaskiya, da sadaukarwa amma a yau ana masa kallon dan fashin daji, makashi, mai fyade, barawon shanu da mai garkuwa.”