Adadin Karin Kudin Lambar Mota da Lasisin Tuki da Gwamnatin Tarayya ta yi
Kaduna – Wani rahoton ThePunch ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da karin kudin lambar mota da kuma lasisin tuki a fadin Najeriya.
Rahoton ya nuna cewa hukumar haraji JTB ta yanke shawaran ne a ganawarta ta 147 da akayi a Kaduna ranar Alhamis, 25 ga Maris. Legit.ng ta tattaro cewa JTB ta aika wasikar aiwatar da umurnin ranar Juma’a, 30 ga Yuli ga dukkan hukumomi a jahohi da tarayya.
A cewar wasikar, shugaban JTB yace a fara aiwatar da sabon farashin ranar 1 ga agusta.
Shugaban hukumar haraji ta kasa FIRS ke jagorancin JTB.
Ga jerin sabbin farashin da aka sa:
Lambar Mota:
Read Also:
Standard private and commercial number plates Motocin haya da marasa haya – (Sabon farashi: N18,750; Tsohon farashi: N12,500)
Lambar mota na gayu – (Sabon farashi: N200,000; Tsohon farashi: N80,000).
Lambar babur – (Sabon farashi: N5,000; Tsohon farashi: N300).
Lamba na musamman – (guda uku) – (Sabon farashi: N30,000; Tsohon farashi: N2,000).
Lambar mota na daban – (Sabon farashi: N50,000; Tsohon farashi: N40, 000).
Lambar motar gwamnati – (Sabon farashi: N20,000; Tsohon farashi: N15,000)
Lasisin Tuki
Lasisin mota (shekara uku) – (Sabon farashi: N10,750; Tsohon farashi: N60,000)
Lasisin motta (Shekara biyar) – (Sabon farashi: N15,000; Tsohon farashi: N10,000)
Lasisin Babur/Keke Napep (shekara 3) – (Sabon farashi: N5000; Tsohon farashi: N3000)
Lasisin Babur/Keke Napep (shekara 5) – (Sabon farashi: N8000; Tsohon farashi: N5,000)